Labaran Kano
Rikicin masarautar Kano na dab da warwarewa – Gwamna Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ana samun karuwar fahimtar juna a siyasar jihar, tare da fatan rikicin masarautar Kano zai warware cikin lumana.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne yayin wani taron addu’o’i da karatun Al-Kur’ani a gidan gwamnati, inda mahalarta suka yi addu’ar zaman lafiya da hadin kai.
Gwamnan ya ce halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, a wasu taruka alama ce ta ingantuwar dangantaka ta siyasa.
Ya kuma bukaci ‘yan siyasa su guji siyasar gaba da gaba, tare da jaddada kudurin gwamnati na yaki da daba da kuma aiwatar da ayyukan raya jama’a.
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya bukaci al’umma su ci gaba da addu’a domin zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.
You must be logged in to post a comment Login