Labarai
Rikicin shugabanci: Ganduje ya rattaba hannu ga dokar Kantin Kwari
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Sanya hannu akan dokar tafiyar da kasuwanci a Kantin kwari, wadda zata tabbatar da gudanar da kasuwancin bisa ka’ida.
Ganduje ya Sanya hannu a dokar ne a yayin zaman majalisar zartarwa a ranar larabar nan, 3 ga watan Nuwanba.
Da yake zantawa da Freedom Radio Kwamishinan Sharia na jihar Kano Barrister Musa Abdullahi Lawan ya ce dokar zata taimaka wajen samarwa gwamnatin jihar kano kudaden shiga da magance rigingimun shugabanci a kasuwar ta Kantin kwari.
A wani labarin kuma, Gwamna Ganduje ya sanya hannu akan dokar da za ta rika tafiyar da ayyukan hukumar yawon bude idanu, inda Kwamishinan na shari’ah ya ce dokar zata taimaka wajen riƙa tafiya da zamani Wanda zai ƙara kawo wa jihar ta kano kudaden shiga
Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Kuma sanya hannu akan dokar da aka gyara ta majalisar wayar da kan jamaa wato community reorientation council law amendment
You must be logged in to post a comment Login