Labarai
Rufe wajan hakar ma’adanai a jihar Kebbi zai taimaka wajan rashin tsaro
Kimanin masu hakar ma’adanai 156’000 ne suka rasa aikin yinsu a jihar Kebbi sakamakon rufe wuraren da Hukumar ‘yan sanda tayi watanni uku da suka huce.
Rahotanni na nuna cewar rufe wuraren hakar ma’adainai a Birnin Kebbi zai taka mihimmiyar rawa wajan kara samun marasa aikinyi a fadin kasar nan duba da kimanin mutanen 156’000 dake sana’ar da ita suke daukar nauyin kansu da na iyalam su.
Shugaban cibiyar bunkasa fasahar zamani da wayar da kan al’umma wato CITAD Yunusa Zakari Ya’u ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da manema labarai kan halin da masu hako ma’adanai suke ciki kimanin watanni uku.
Yunusa Zakari Ya’u yace a wani bincike da suka gudanar ya nuna cewar masu hakar ma’adanan a jihar ta Kebbi suna yin sana’ar su bisa ka’ida duba da duk wanda suke sana’ar sunada rista
Yace Hukumar ‘yan sandan kasar nan bai kamata ta dauki Matakin data daukaba na rufe wurare hakar ma’adanan saboda akwai Hukumar da suke karka shinta.
Cibiyar ta CITAD ta yi kira ga mahukunta dasu duba lamarin kafin ya kai ga masu hakar ma’adanan sun kai ga daukan wani mataki.