Kiwon Lafiya
Rundanar yan sanda Taraba ta tabbatar da mutuwa wani dan Majalisar Takum
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar wani dan majalisa da ke wakiltar Takum I a majalisar dokokin jihar Taraba mai suna Hosea Ibi da masu garkuwa da mutane suka kashe, bayan da suka sace shi a gidan sa da ke daura da barikin Ada a karamar hukumar Takum.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ASP David Mishar ne ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa samun gawar dan majalisar na neman tayar da rikici a yankin karamar hukumar ta Takum, inda matasan yankin ke zargin hukumomin tsaro da gaza tabuka abin azo a gani wajen kubutar da marigayin, daga hannun masu garkuwar.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewar fusatar da matasan yankin suka yi ka iya tayar da rikcicin da zai iya shafar mutanen da basu ji basu gani ba, inda suka bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakan da suka dace, domin hana tashin rikicin, sakamakon mutuwar dan majalisar.
Rahotanni sun bayyana cewa ranar 30 ga watan da ya gabata ne na Disamba masu garkuwa da mutanen suka sace dan majalisar Hosea Ibi a gidan sa da ke Takum.