Labarai
Rundunar ƴansandan Kano ta buƙaci jami’anta su tsananta sanya idanu a kan iyakokin jihar

Rundunar ƴansandan jhar Kano ta buƙaci jami’anta su tsananta sanya idanu a kan iyakokin jihar.
Kwamishin ƴanandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawagar jami’an rundunar zuwa yankunan ƙananan hukumomin Tsanyawa da Shanono da ke kan iyakar jihar da Katsina.
CP Bakori ya buƙaci jami’an tsaron da ke sintiri a yankunan su tsananta sanya idanu da matsin lamba kan miyagun da ke harkokinsu a yankunan domin maido da zaman lafiya.
A baya-bayan nan jihar Kano ta riƙa fuskantar hare-haren ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa a yankunan jihar da suka yi iyaka da Katsina mai fama da hare-hare.
You must be logged in to post a comment Login