Labarai
Rundunar Neighbourhood Watch ta ja hankalin mutane kan daukar matakan kare kai

Rundunar tsaro ta Neighbourhood Watch Corps, watau Rundunar Kula da Unguwanni ta Jihar Kano, ta ja hankalin al’umma da su kasance masu sanya ido tare da sanin mutanen da suke mu’amala da su a cikin unguwanninsu, domin ƙara ƙarfafa tsaro a fadin jihar.
Babban Kwamandan Rundunar Aminu Yusuf Abdulmalik, ne ya y wannan jan hankali a hirarsa da Freedom Radio.
Ya ce, wajibi ne kowane mutum ya bayar da gudummawa wajen samar da tsaro mai ɗorewa a fadin jihar Kano.
A cewarsa, tsaro ba na gwamnati kaɗai ba ne, al’umma na da rawar da za su taka ta hanyar bayar da bayanai da kuma haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
You must be logged in to post a comment Login