Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muhammad Hussain Gumel ya kama aiki a matsayin sabon kwamishinan yan sandan Kano

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano, a bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da fita domin kada kuri’ar a zaben gwamna ba tare da wata fargaba ba.

Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Hussain Gumel,ne ya bukaci hakan yayin ganawarsa da manema labarai da safiyar yau Alhamis.

Muhammad Hussain Gumel na wannan jawabi ne jim kadan bayan isowarsa Kano a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda.

Haka kuma ya kara da cewa, sun shirya tsaf domin bayar da ingantaccen tsaro a fadin jihar Kano.

A cewarsa babu yadda za a yi al’umma su ci gaba matukar rundunar ba ta bayar da gudunmawar zaman lafiya ba, don kuwa rashin tsaro babbar illa ce tare da barazana.

Hussain Gumel ya kuma ce, rundunar ta shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazanar rashin tsaro da ka iya tasowa domin tabbatar da ganin ta murkushe masu tayar da hankalin al’umma.

Haka kuma yace ba zasu kyale masu kokarin satar akwatu ko kuma fasa su ba a ranar zaben gwamna da yan majalisar dokokin jiha da ke tafe.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!