Kiwon Lafiya
Rundunar soja ta mikawa gwamnatin Borno ‘yar Chibok din da suka ceto a baya-baya nan
Rundunar sojin kasar nan ta mikawa gwamnatin jihar Borno daya daga cikin daliban makarantar sakandiren Chibok, mai suna Salomi Pogu wadda suka samu nasarar ceto daga hannun mayakan Boko Haram, a baya-bayan nan.
Da yake mika yan matan biyu ga mataimakin gwamnan jihar Usman Durkwa a birnin Maidugurin jihar Borno, kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Rogers Nicholas yace sun samu nasarar ceto Salomi Pogu ranar 4 ga watan Janairu tare da Jamila Adams a garin Pulka da ke yankin karamar hukumar Gwoza.
Mista Nicholas ya kuma bukaci gwamnatin jihar da tayi yan matan biyu rijista, kamar yanda aka yiwa sauran ‘yan matan da aka ceto a baya, kafin mika su hannun iyayen su.
Da yake jawabi, mataimakin gwamnan jihar Borno Usman Durkwa ya yabawa rundunar ta Operation Lafiya dole bisa irin rawar da ta taka wajen ceto ‘yan matan, da kuma irin namijin kokarin da takeyi wajen yakar yan tada kayar bayan.
Usman Durkwa ya bayyana fatan sa na ganin cewar an samu nasarar ceto sauran ‘yan matan da ke hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
A shekarar 2014 ne kungiyar ta Boko Haram ta sace yan matan sakandiren Chibok su dari biyu da goma sha tara.