Kiwon Lafiya
Rundunar sojan kasar nan tayi sauyin ma’aikata don tabbatar da daidaito
Rundunar sojin saman kasar nan ta ce ta sake sauyawa wasu daga cikin manyan jami’anta wurare aiki daban-daban a fadin kasar nan domin tabbatar da daidaito a cikin ayyukan rundunar.
A cewar rundunar sauya wuraren aikin ya shafi air vice marshal goma 16 da kuma commoders 16 da kuma group captain guda tara sai kuma squadron guda hudu.
Wanan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin saman kasar nan AVM Olatokumbo Adesanya ya fitar.
Adesanya ya ce fitattu cikin wadanda al’amarin ya shafa sun hadar da Shugabanin rassan rundunar guda hudu dake shalkwatar ta a birinin tarayya Abuja da kuma bababn kwamada da ke bada umarni ga zirga-zirgar jiragen sama a rundunar.
Haka kuma sanarwar ta ce sauye-sauyen ya kuma shafi nada wasu a mukamai daban-daban awani bangare na tabbatar da gaskiya da adalci da kuma hana wasu dadewa a ofishi guda ta yadda za a tabbatar