Labarai
Rundunar Soji ta gargadi Mutane game da shafukan sada zumunta na bogi

Rundunar Sojin Kasar nan ta gargadi jama’a game da shafukan sada zumunta na bogi da ke ikirarin cewa Babban Hafsan Sojan Kasa , Laftanar Janar Waidi Shaibu ne ke gudanar da su.
Mukaddashin Darakta, Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin, Kanar Apoloniya Anele, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abuja a yau Juma’a.
Kanar Apoloniya Anele ya ce rundunar sojin ta lura da karuwar asusun yanar gizo na zamba da mutane marasa imani ke kirkira da sunan damfarar jama’a.
You must be logged in to post a comment Login