Kiwon Lafiya
Rundunar sojin kasar nan ta bukaci yan Nijeriya da su taimakawa yan Arewa maso gabashin kasar nan
Rundunar Sojin kasar nan ta bukaci kungiyoyin jin-kai da su tallafawa al’ummar yankin Arewa Maso gabashin kasar nan da rikici ya raba da gidajensu, wadanda suka koma gida.
Babban Hafsan Sojin kasa na kasar nan Laftanar Janar Tukur Buratai ne ya yi wannan kira jiya, ta-bakin wakilinsa Manjo Janar David Ahmadu, inda ya bada tabbacin samar da ingantaccen tsaro ga ‘yan gudun hijirar da suka koma gida.
Cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labaran rundunar Sojin kasar nan Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayar, ta ce shi ma kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole Manjo Janar Rogers Nicholas ya bi sahun Janar Buratai wajen nemawa ‘yan gudun hijirar da suka koma garinsu na Gudunbali a Jihar Borno.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun Soin sun gudanar da binciken gida-gida da kuma gonaki don tabbatar da tsaro a yankin gabanin komawar ‘yan gudun hijirar.
Haka zalika Janar Buratai ya kaddamar da wani aiki na kammala samar da tsaro a Munguno a Jihar ta Borno, bayan bude Ofishin rundunar a barikin Kinasara, tare da mika tuta ga kwamandan rundunar Manjo Janar Abbas Dikko.