Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Rundunar sojin kasar nan ta sanar da ‘yantar da fiye da mutane dubu goma

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta sanar da cewa ta ‘yantar da fiye da mutane dubu guda daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayar a jiya Litinin, inda ya ce dakarunsu na  shiyya ta 22 tare da hadin giwar rundunar Lafiya Dole suka samu nasarar ceto mutanen.

Sannan ya kuma ce sun samu hadin kan dakarun tsaro na kasa-da-kasa na Multintional Joint Task Force yayin aikin.

Janar Texas Chukwu ya kara da cewa an ceto mutanen daga kauyukan Malamkari da Amchaka da Walasa da kuma Gora, dukkansu cikin karamar hukumar Bama a Jihar Borno.

Mafi-akasarinsu dai mata ne da kananan yara tare kuma da wasu matasa da aka tilastawa shiga kungiyar ta Boko Haram.

Birgediya Janar Texas Chukwu ya nanata kudurin rundunar Sojin kasar nan wajen kakkabe duk wani nau’I na ta’addanci a yankin na Arewa Maso Gabas da ma kasa baki-daya, tare da ceto mutanen da ke hannun mayakan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!