Labarai
Rundunar sojin Najeriya da hadin gwiwar takwarorinta na makwabtan kasashe sun kai farmaki kan shugabannin Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya da hadin gwiwar takwarorin su na makwabtan kasashe sun kaddamar da gagarumin farmaki kan shugabannin bangarorin kungiyar Boko Haram biyu a Talatar nan.
Dakarun daga kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya na farautar Abubakar Shekau a cikin dajin Sambisa da Mamman Nur a cikin Tafkin Chadi domin murkushe su.
Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta ce an kashe mayakan kungiyar ta Boko Haram masu yawan gaske a sabon farmakin da dakarun suka kaddamar.
Birgediya janar Sani Usman Kuka sheka ya ce matakin na sojin da aka yiwa lakabi da farmakin ganin kwa-kwab kashi na biyu na samun gagarumar nasara.
To amma ya ce hudu daga cikin dakarun su sun kwanta dama tara kuma sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake na mota a kusa da sansanin Abubakar Shekau a jiya litinin.
To amma wasu majiyoyin soji dana civilian JTF sun shedawa manema labarai cewar sojin da suka mutu sun kai goma.
Hukumomin sojin Kamaru kuwa sun ce sojin su biyu sun mutu a Dajin Sambisa to amma babu tabbas ko suna cikin wadanda Birgediya Janar Kuka Sheka ya ambata.
Sanarwar har ila yau ta ce sabon farmakin dakarun hadin gwiwar na samun gagarumar nasara a yunkurin murkushe mayakan kungiyar ta Boko Haram.
A kwanakin baya ma rundunar ta kaddamar da wani farmaki kan mayakan kungiyar inda suka ce an raunata Mamman Nur yayin fafatawar.