Labarai
TSARO: Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/08/sojoji.jpg)
Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce dakarun Operation wutar tabki na rundunar sojin kasar nan sun kashe ‘yan boko haram da ‘yan kungiyar ISWAP da dama a yankin tabkin Chadi.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa manjo janar John Enenche ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce jiragen yakin dakarun ne suka yi luguden wuta kan maboyar ‘yan ta’addar a kauyukan Tundun Wulgo da Tumbun Gini da ke daf da tabkin Chadi.
Haka zalika sanarwar ta kuma ce an kai harin ne a ranar Alhamis din da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login