Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta nada wasu manyan hafsoshi da za su kula da wasu sassan kasar
Rundunar sojin kasar nan ta ce ta nada wasu daga cikin manyan hafsoshi wadanda za su rika kula da wasu sassan kasar nan daga shalkawatar tsaro ta kasa.
Haka kuma a cewar rundunar ta tura wasu daga cikin hafsoshi zuwa wasu yankuna na kasar nan domin kula da yadda lamuran zaben ke gudana.
Mai magana da yawun rundanar sojin kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa.
Wasu daga cikin hafsoshin da aka daura musu nauyin kula da ayyukan sun hada da: Manjo janar Oga Adeniyi wanda yake a matsayin babban kwamandan lafiya dole dake yaki da ayyukan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, sai Manjo Janar ECN Obi daga shalkwarta tsaro ta kasa.
Sauran sun hada da: Manjor Janar LF Abdullahi, da Burgediya janar GK Nwosu da Burgediya janar CA Apere da Burgediya janar K.I. Yusuf da Burgediya janar S.S Araoye da kanal D.C Bako da kuma kanal L.G Lepdung.