Connect with us

Labarai

Rundunar sojin Najeriya ta tura dakaru jihar Filato don daƙile ayyukan yan bindiga

Published

on

Rundunar sojin Najeriya, ta sanar da tura dakaru na musamman zuwa jihar Filato domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da kuma fuskantar sabon ɓarkewar hare-haren rashin tsaro a jihar.

 

Matakin ya biyo bayan amincewar da Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bayar na tura Rundunar ta musamman zuwa yankin.

 

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “dakarun sun  isa Jihar Filato,  kana za su gudanar da ayyuka na murkushe ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

 

Yayin karɓar dakarun a hedikwatar Rundunar Soji ta 3 Division, babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Folusho Oyinlola ya yaba da jagorancin gaggawa da Shugaban Sojin Kasa ya nuna wajen samar da muhimman kayan yaƙi da sauran kayayyakin aiki da za su ba dakarun damar aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!