Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kotu ta dakatar tsige mataimakin gwamnan jihar Imo

Published

on

Mai shari’a Ben Iheka na babbar kotun jihar Imo ya dakatar kwamitin da babban jojin jihar Paschal Nnadi ya kafa da kuma shugaban majalisar dokokin jihar AchoIhim, daga daukar matakin tsige mataimakin gwamnan jihar Eze Madumere, har sai ya kammala sauraron karar.

Mai shari’a Ben Iheka ya bayyana hakan ne a yau Litinin cikin wani umar ni da ya bayar.

Rahotanni sun ce babban jojin jihar ta Imo ne ya kafa kwamitin domin gudanar da bincike kan zargin da majalisar dokokin jihar kewa mataimakin gwamnan na rashin da’a.

Mai shari’a Iheka ya kuma bada umarci mambobi uku na kwamitin su dasu girmama wannan umarni na kotu da ya dakatar da yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

Lauyan mataimakin gwamnan Ken Njemanze ya shedawa kotun cewar a shirye suke su bawa kotun hadin kai ta gudanar da shari’a kan wannan yunkuri na tsige shi daga mukamin sa.

Ya ce sun dogara da kotun cewar zata yi adalci domin kare mutuncin lamba biyun na jihar Imo da kuma martabar ofishin mataimakin gwamna.

Bayan sauraron lauyan ne kuma mai shari’a Ben Iheka ya amince da bukatar mai kara, sannan ya dage zaman zuwa 13 ga watan gobe.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!