Kiwon Lafiya
Rundunar sojin Nijeriya ta mayar da martani dangane da harin boko haram a Borno
Rundunar sojan kasar nan ta maida martani kan harin da wani dan kungiyar Boko Haram yayi badda-kama a matsayin ma’aikacin bada agajin jin kai ayankin Gudinbali dake jihar Borno.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mataimakin rundunar yaki ta Operation Lafiya Dole Kanal Onyema Nwachukwi ya fitar a jiya Lahadi cewa tun a ranar 14 da wannan watan ya shiga yankin yana amfani da sunan cewa shi ma’aikacin bada agaji ne. Onyema Nwachukwu ya ce dan kunar bakin waken yayi amfani da sunan ne, ta wajen raraba kayayyakin jin kai ga al’ummar yankin yayin da ya bude wuta ka jami’an tsaro da sojojin dake kan aiki