Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An nada Sarkin Dutse Alh. Nuhu Muhammad Sanusi a matsayin uban jami’ar jihar Sokoto

Published

on

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya nada Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi a matsayin uban jami’ar Jihar Sokoto.

An yi nadin ne a jiya asabar 13 ga watan Maris lokacin bikin yaye daliban jami’ar, inda kuma aka sanyawa ginin majalisar dattijan jami’ar sunan marigayi Alhaji Umaru Ali Shinkafi, sai kuma dakin karatun jami’ar da aka sanyawa sunan marigayi Inuwa Abdulkadir.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce ilimi shi ne jigon ci gaban ko wace al’umma, a don haka gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen sanya kashi 26 na kasafin kudin ko wace shekarar.

Ya kara da cewa ko a shekarar 2016 sai da ya ware kashi 29 cikin dari a matsayin kasafin kudin ma’aikatar ilimin, wanda ma ya zarta yadda hukumar raya ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta tsara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!