Labarai
Rundunar sojin sama a Najeriya sun kashe ‘yan fashin daji a jihar Zamfara

Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yanfashi da dama a garin Tsafe na jihar Zamfara bayan yi musu kwantan bauna ta hanyar amfani da jiragen yaki ta sama.
Mai magana da yawun rundunar,,Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai hare-haren ne kan sansanin ‘yanfashin a ranar Juma’a 14 ga watan Nuwamba 2025 bayan tattara bayanan siri da suka samu.
Ya ce bayanai sun tabbatar da ‘yanbindigar na karakaina a wurin da suka ɓoye shanun sata da ke kan wani tsauni da ke ba su kariya da kuma ajiye kayayyaki.
“An kai hare-hare da dama waɗanda suka dira kan ‘yanfashin da ke yunƙurin guduwa cikin duhun daji, inda aka bi su kuma aka kashe su,” in ji sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login