Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar sojojin sama ta hallaka kwamandodin ‘yanbindiga biyar a Zamfara

Published

on

Rundunar sojojin saman kasar nan samu nasarar hallaka manyan kwamandodi biyar na ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Rundunar ta samu wannan nasara ne bayan wani sumame da ta kai dazuzzukan da ‘yan bindigar ke boye a Jihohin Arewa maso Yamma.

Manyan kwamandodin da aka kashe, sune Hussaini Rabe, da Murtala Sabe, da Basiru Nasiru, da Sama da kuma Isah.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaye sunan sa yace lugudan wutar da sojin saman suka yi a Dajin Tsaunin Sani da ke gundumar ‘Yantumaki ta karamar Hukumar Danmusa, a jihar Katsina ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan bindiga sama da 26, tare da lalata babura 13.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!