Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta ce sanarwar harin kisan da majalisar dattawa ta ce an kaiwa Sanata Ike Ekweremadu ba gaskiya bane
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce ba gaskiya bane sanarwar da majalisar dattawa ta fitar cewa ‘yan ina da kisa ne suka yi yunkurin kashe mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu a gidan sa da ke Abuja.
Mai magana da yawun rundunar Jimoh Moshood ya shaidawa manema labarai cewa sun kama wani mutum da ake zargin ya shiga gidan mataimakin shugaban majalisar don yin sata ba don kashe shi ba, mai suna Muhammed Yusuf, dan asalin karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.
Haka kuma ya ce akwai wani mutum da ya taimaka masa mai suna Ali wanda yanzu rundunar ke neman sa ruwa a jallo.
A cewar mai magana da yawun rundunar wanda ake zargin ya kuma shiga gidan wani mutum mai suna Halliru Adamu da ke Dennis Osadebey Crescent daf da gidan mataimakin shugaban majalisar, inda ya saci wayoyin hannu da gwala-gwalai da kuma wasu kayayyaki da dama.
Mai Magana da yawun rundunar ya kuma bukaci jama’ar kasar nan da su rika barin jami’an tsaro suna gudanar da aikin su a duk lokacin da lamarin makamancin wannan ya faru.