Kiwon Lafiya
Rundunar ‘Yan sanda ta kubutar da ‘Yan Afrika ta Kudu biyu da aka sace su a Kaduna
Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta ce ta kubutar da wasu ‘Yan kasar Afrika ta Kudu biyu da aka sace su a wani wurin aikin hakar ma’adinai cikin kauyen Maidaro a jihar Kaduna.
Wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jimoh Mashood ya fitar, ta ce sai da jami’an tsaro suka yi amfani da jirgi mai saukar Ungulu da wasu ‘yan sanda na musamman kafin cimma sako mutanen guda biyu.
Mutanen da aka kubutar sun hada da Thomas Arnold Pearce da Mista Hendrik Gideon bayan sace su a ranar Talata 23 ga watan Janairun da muke ciki a kauyen Maidaro.
Sanarwar kuma ta ce an sako mutanen ne a jiya Asabar ba tare da wani rauni a jikin su ba.
Sai dai rundunar ‘yan sandan ba ta yi bayani ba ko sai da aka biya kudin fansa kafin a sake su.
Al’amarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan kubutar da wasu turawa ‘yan Amurka biyu da kuma ‘yan Canada biyu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.