Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An yi wa Sule Lamido gwajin Coronavirus

Published

on

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da wasu makunsantansa sun kai kansu cibiyar gwajin cutar Covid-19 da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano, biyo bayan mu’amala da ake kyautata zaton sun yi da mai dauke da Cutar a nan Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa Alhaji Sule Lamido da ma dinbin jama’a sun halarci wani taron janaiza a Unguwar Koki a ranar alhamis din da ta gabata, inda mai dauke da cutar ya yi mu’amala da mutane da dama.

LABARAI MASU ALAKA

Covid -19: Shugaba Buhari zai yi jawabi akan Corona

Ganduje ya tabbatar da bullar cutar Corona a Kano

Da Dumi-Dumi: An samu bullar Corona Virus a Kano

Kwamitin kai ta kwana kan yaki da cutar Covid-19 na Jihar Kano ne ya aikewa tsohon gwamnan da ma wasu mutane sako da ke shawartarsu da su je a gwada su don sanin matakin lafiyarsu.

Sakataren kwamitin wanda kuma shi ne daraktan sashen kula da lafiyar al’umma na ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano Dakta  Imam Wada Bello, ya tabbatarwa Freedom Radio da yammacin yau cewa ba wai Alhaji Sule Lamido kadai suka gayyata ba, har ma da wasu mutanea nan Kano da ake kyautata zaton sun yi mu’amala da mai dauke da cutar ta Covid-19 a nan Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!