Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano ta magantu dangane da gobarar data tashi a Sharkwatar

Published

on

  • SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ‘ gobarar bata shafi ofishin kwamishin ‘yan Sandan da kuma dakunan da ake ajiye masu laifi’.
  • Wanda ya ce ‘ana zargin wayar wuta ce ta haddasa gobarar’.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta ce ‘gobarar da ta tashi jiya a shalkwatarta da ke Unguwar Bompai ba ta shafi ofishin kwamishina da Kuma inda ake tsare da wadanda ake zargi da aikata Laifuka ba’.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan ga Freedom radio a daren jiya Asabar.

Kiyawa yace ‘gobarar ta kone ofisoshi masu tarin Yawa da ke bene hawa na daya a Shelkwatar’.

Wanda yace ‘muna zargin gobarar ta tashi ne sakamakon hadewar wasu wayoyi na lantarki, Amma duk da haka ana nan ana cigaba da bincike’.

RAHOTO: Abba Isa Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!