Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda sun kama mutane 4 bisa yunkurin kona ofishin INEC na Takai

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta kama mutane huɗu da take zargi da yunkurin ƙona ofishin hukumar zaɓe a karamar hukumar Takai.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a jiya Lahadi.

Ya ce, ana zargin mutane huɗun da yunkurin ƙona ofishin hukumar ta INEC a daidai lokacin da ake sanar da sakamakon zaɓe.

Haka kuma DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kuma ce, rundunar ta kama wasu ƴan bangar siyasa da suka kai hari ofishin yakin neman zaɓe na jam’iyyar NNPP a karamar hukumar Tudun Wada, inda suka kashe mutum biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!