Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kai ziyarar ta’aziya gidan wanda jami’insu ya harbe

Published

on

Tawagar rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyaye da kuma ‘yan uwan marigayi Salisu Rabiu da akafi sani da Salisu Player dake Unguwar Kurna dake yankin karamar hukumar Fagge.

Tawagar rundunar a karkashin jagorancin mataimakin Kwamishinan yan sanda DCP Umar Ahmad Chusu da sauran manyan jami’an yan sandan Kano sune suka je gidan su marigayin Salisu domin yi musu ta’aziyyar mamacin da wani dan sandan rundunar ya harbe da bindiga abaya – bayan nan.

Tawagar yan sandan a karkashin DCP Umar Ahmad Chusu sanye da kayan gida wanda hakan ke nuna alhinin rundunar bisa ga rasuwar marigayi Salisu Rabiu player.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi HarunaKiyawa ya turawa Freedom Radio ya ce, ‘anyi addu’oi na musamman ga marigayin tare da baiwa yan uwan marigayin Salisu hakuri bisa iftila’in daya faru wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar marigayin Salisu Player a baya – bayan nan’.

Freedom Radio ta rawaito cewa ‘rundunar ta kuma tabbatarwa da ‘yan uwan marigayi Salisu cewa zata hukunta wanda ake zargi da laifin harbe marigayi Salisu wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa’.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!