Labaran Kano
Rundunar Yan sanda ta kama jabun kudade da aka shigo da su jihar Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu bata gari da suka shigo da miliyoyin kudi Jihar na jabu domin amfani dasu wajen Damfarar mutane musamman ‘yan kasuwa.
Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da Freedom Radio.
Ya Kuma bukaci ‘yan kasuwa da su lura da kudaden da mutane za suzo dasu gare su domin yin siyayya dan gudun fadawa hannun batagari.
Kazalika ya ce dalolin Amurka sunfi Yawa a cikin jabun kudaden da aka kama.
You must be logged in to post a comment Login