Connect with us

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kasar nan ta ce ta yi nasarar kuɓutar da mutane 73 da akayi garkuwa dasu a jihar Katsina

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Kasar nan ta ce ta yi nasarar kuɓutar da mutum 73 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu 175 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin jihar Katsina.

A cewar rundunar, an kama mutum 15 da ake zargi da aikata laifin fashi da makami, daya kuma an kama shi da laifin yin garkuwa da mutane, sannan an kama wasu 20 wadanda ke gidan yari bisa laifin kisa.

Kazalika, an kama daya da ake zargi da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba, yayin da wasu talatin ke da alaka da laifukan fyaɗe.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq, ya fitar, ya bayyana ci gaban a matsayin wani bangare na nasarorin da rundunar ta samu a watan Mayun 2025.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da bindiga kirar AK-49 kuma wata ƙaramar bindigar hannu guda ɗaya, da harsashi mai tsawon mita ɗari biyar da shida, da babura biyu da ake zargin na sata ne, da kuma dabbobi 174 da ake zargin an sace su.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!