Labarai
Rundunar ‘yan-sandan Najeriya ta tura dakarunta Jihar Benue domin dakile rikice-rikcen Jihar
Rundunar ‘yan-sandan Najeriya ta tura dakarunta kwararru na musamman da aka raba zuwa rukunoni 15 zuwa Jihar Benue domin dakile rikice-rikcen da ke faruwa a Jihar.
Kwamishinan ‘yan-sandan Jihar ta Benue Fatai Owoseni ya bayyana cewa Babban Sufeton ‘yan-sandan kasar nan Ibrahim Idris ne ya bada umarnin girke jami’an, inda ya sanar da cewa sun ceto wani jami’insu da ya yi batan dabo lokacin da aka kai hari a kananan hukumomin Yogbo da Guma a Jihar.
Ya kara da cewa an rarraba jami’an a yankunan Kwande da Agatu da Makurdi da Buruku da Katsina-Ala da Gwer ta Yamma da kua Vandeikya.
Haka zalika ya shaida cewa jami’an na su sun zamu zarafin fatattakar masu kai hare-haren inda zaman alfiya ya fara samuwa a Jihar Benue.