Labarai
Rusau a Kano ka iya jawo koma bayan tattalin arzikin jihar- Dakta Abdussalam Kani
Masanin tattalin arzikin a jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Dakta Abdussalam Muhammad Kani, ya yi hasashen cewa, rusau da gwamnatin Kano ke yi a wuraren da aka gina ba bisa ka’ida ba, ka iya mayar da tattalin arziki baya.
Dakta Abdussalam Muhammad Kani ya ce, ’akwai barazanar sanya tsoro a zukatan masu sha’awar zuba hannun jari a Kano’.
Haka zalika Dakta Abdussalam Muhammad Kani ya kara da cewa ‘bayan sanya tsoro ga masu son zuba hannun jari, akwai karuwar marasa aikin yi a Jihar duba da cewa yawancin inda aka rushe wuraren kasuwanci ne’.
Abdussalam Kani ya kuma ce wadannan matsalolin zasu kawo koma bayan samar da kudin haraji daga wadanda akayiwa rusau din, wanda hakam zai ragewa gwamnatin samun kudaden shiga, da zai iya hana biyan kudaden bashin da ake bin jihar, tare da hana wadanda suke bayar da bashin su cigaba da bawa jihar.
‘Ya kamata gwamnatin idan ta samu kamar shagunan da akayi a gaban asibitoci a rufesu ta waje a bude ta ciki a cigaba da amfani dasu a matsayin shaguna, inda idan aka samu shuganan da akayi a gaban asibiti, a mayar dasu cikin asibitin a cigaba da amfani dashi a ciki,
Ya kuma ce ‘kamar a otal din Daula kamata yayi a mayarwa da makarantar a aka karba, daliban su cigaba da amfani dashi kamar da’.
A don hakan ya ce ‘idan har gwamnatin zatabi matakan shari’a yayin rusau din, yins aba matsala bane, inda ai matakan shari’a a kwace wurin, inda ta tabbatata za’a rushe a rushe din, a inda zaa samu maslahar al’umma, sai gwamnati ta tsaya ta kalla’.
You must be logged in to post a comment Login