Labarai
Rusau : Gwamnati ta shiga tsakani kan rikici a kasuwar Kurmi – Mahauta
Daga Bilal Nasidi Ma’azu
Mahautan dake Kasuwar Kurmi cikin karamar hakumar birni sun bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a nan Kano,dasu sanya baki,kan rushe musu runfunansu a kasuwar ,wanda suka ce shugabancin karamar hukumar ta Birnin Kano ya fara gabatarwa a jiya Laraba.
A cewar Mahautan sama da shekaru 100 suka mallaki runfunan tin iyaye da kakanni,amma lokaci daya aka basu umarnin tashi daga runfunan.
Ce-cekucen ‘yan kasuwar kenan a yayin da shugabacin karamar hukumar birnin ke rushe musu runfunan nasu a kasuawar a jiya Labara.
Wasu mahauta da freedom rediyo ta zanta dasu,sun bayyana cewa shugaban kasuwar Alhaji Alhassan Tanko ya aike musu da sanarwar cewa zata fara rushe runfanan nasu,to sai kuma ‘yan kasuwar sun ce runfanan fa mallakin su,bana karamar hukuma ba ne.
Jin koken ‘yan kasuwar ne ya sanya muka tuntubar shugaban Mahautan na karamar hukumar birnin domin tabakinsa kan batun,to sai dai muntarar da ofishinsa a garkame,hakanne ya sanya muka tuntubeshi ta wayar tarho wanda a karshe hakan mu bai cimma ruwa
Dalilin kenan da ya sanya muka nemi jin tabakin shugaban kungiyar Mahauta ta kasa reshen jihar Kano, domin jin inda aka kwana game da wannan turka-turka.
Alhaji Shehu Malanta shi ne shugaban kungiyar Mahautan yayi karin haske game da lamarin game da makomar ‘yan kasuwar.
Alhaji Dan Bello Aminu shi ne Mataimakin Shugaban Haramar hukumar Birnin Kano,na kuma tambayeshi ko me mai zai ce game da rushe runfunan mahautan a jiya.
Mahautan dai sun bukaci gwamnatin data yiwa All.. ta sanya baki kan rushe musu runfunan nasu a kasuwar wanda shugabancin Karamar hukumar ya fara gudanarwa a Ranar Labara.
You must be logged in to post a comment Login