Labarai
Saɓa dokar aiki: KAROTA ta kori wani jami’inta
Hukumar KAROTA ta kori wani jami’inta mai suna Jamilu Gambo.
Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗan-agundi ne ya bada umarnin korar jami’in sakamakon kama shi da laifin karya dokar aiki.
Tun da fari jami’in an kama shi da laifin fasawa wani direban babbar mota tayar sa a ranar Laraba a titin zuwa Haɗijia.
Hukumar ta ce, laifin da ya aikata ya saɓa doka, kuma hukuncin shi ne abinda ya dace biyo bayan zaman yarjejeniyar da aka yi kuma aka yanke hukuncin cewa “Duk jami’in da aka kama da laifin rashin ɗa’a da kuma saɓa doka to kuwa za a kore shi nan ta ke”.
“Abin da jami’in ya aikata ya nuna ƙarara ba shi da ƙwarewa kuma ba shi da ɗa’a, kuma wannan misali ne ga duk jami’in da ke shirin aikata makamancin wannan laifi”.
Wannan na cikin wani saƙon murya da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabulusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya aikowa da Freedom Radio.
Sakon ya kuma ce, ba iya jami’an KAROTA kaɗai dokar ta shafa ba, domin kuwa duk wani jami’i mai kaki da aka kama da laifin zai karɓi irin hukuncin.
You must be logged in to post a comment Login