Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yanke hukuncin kisan kai ga wani matashi a nan kano

Published

on

Babbar kotun jiha da ke zaman ta a Audu Bako sakateriya karkashin jagorancin Ahmadu Tijjani Badamasi ya yanke hukuncin kisan kai ta hanyar rataya  ga wai matashi mai suna Abba Mustapha da ke garin Mailari  Gaidam a garin Uran dake karamar hukumar Gezawa .

 

Wannan laifi dai ya sabawa kundin penal kotu na sashe na 20021 .

 

A ranar daya ga wata Afriru a 2017 ne aka kama matashin da laifin kisan kai ga wani matashi  mai suna Buhari Abubakar wanda ya dauke fatanya yana dukansa a ka har sai da ya kai shi kasa wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar matashin.

 

Lokacin da aka karanta masa laifin nasa matashin ya amince da aikata laifi wanda tun daga wannan lokaci ne ake kulle shi a gidan kaso .

 

Da aka fara sharia mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnati barista Zakariya Yau Muhammad Garba ya gabatar da shaidu guda biyar , sannan lauyan wanda ake tuhumma mai suna Asmau Muhmmad Suleman , wanda ita ce lauyan wanda aka kariya wanda ake tuhuma ya kare kansa.

 

A wani labarin kuma Justice Aishatu Rabiu Danlami Muhammad ta yanke wani matashi dan shekara 37 mazaunin jaen makera quarters  a karamar hukumar Kumbotso mai suna Auwalu Abdullahi a ranar 17 ga watan Yuli 2017 inda ya dauke wani yaro dan shekara 8 zuwa wani kango da aikata laifin hakke masa.

 

Wannan abu dai ya faru ne a unguwar Fulani a Kumbotso wanda ya saba da kundin tsari na sashe 20084 na kundin penal kotu.

 

Da take yanke hukunci mai sharia Aishatu Danlami Muhammad ta ce an samu wannan matashi da laifi dumu-dumu wanda mai gabatar da kara Amina ‘yar Gaya ta gabatar da shedunta guda biyar wanda shedun mai sharia ta ce an gabatar da su sun kuma tabbatar da faruwa abin.

 

An yankewa mai laifin hukuncin shekaru 14 a gidan kaso da aiki mai tsanani da kuma tarar naira dubu hamsi , idan aka gaza biya kuma za’a kara masa shekaru biyu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!