Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Saboda na ki shiga PDP shi ya sa aka dakatar dani daga sarautar wakilin birnin Bauchi

Published

on

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bauchi Yakubu Shehu Abdullahi, ya ce, gwamnan jihar ta Bauchi sanata Bala Abdulkadir Muhammed, shine ya sa aka dakatar da shi daga sarautar wakilin birnin Bauchi saboda kawai yaki amincewa ya shiga jam’iyyar PDP.

 

A baya-bayan nan ne dai masarautar ta Bauchi ta ba da sanarwar dakatar da Yakubu Shehu Abdulahi daga sarautar ta wakilin birnin Bauchi.

 

Sai dai a zantawarsa da manema labarai Yakubu Shehu Abdullahi, ya ce, gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Abdulkadir Muhammed, ya yi zawarcinsa lokacin yana jam’iyyar PRP akan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, inda shi kuma ya ki amincewa da bukatar hakan, maimakon haka sai ya koma jam’iyyar sa ta farko APC.

 

Sai dai da ya ke mai da martani kan kalaman ɗan majalisar, mai bai wa gwmanan Bauchi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya bayyana kalaman ɗan majalisar da cewa shifcin gizo ne

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!