Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasa: Gwamnonin PDP 13 suna gudanar da taron gaggawa a jihar Oyo

Published

on

Gwamnonin jam’iyyar PDP guda goma sha uku sun fara gudanar da wani taro na sirri a birnin Badun na jihar Oyo.

 

Rahotanni sun ce gwamnonin suna gudanar da taron ne a cibiyar kula da harkokin noma a kasashe masu zafi da ke birnin na Badun.

 

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da: Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, Okezie Ikpeazu na Abia, Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom da Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma Duoye Diri na Bayelsa sai kuma Samuel Ortom na jihar Benue.

 

Sauran sune: Ben Ayade na jihar Cross Rivers, Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Godwin Obaseki na Edo, Nyesom Wike na jihar Rivers da Bello Matawalle na jihar Zamfara, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Aliyu Gusau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!