Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Sabon irin waken SAMPEA-20T zai rage giɓin tan dubu ɗari 500 a Najeriya – Nanono

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce sabon nau’in irin wake da ake wa laƙabi da SAMPEA-20T, wadda cibiyar nazari kan harkokin noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a, ta samar, zai taimaka gaya wajen rage giɓin tan dubu ɗari biyar na wake da ƙasar nan ke buƙata.

Ministan aikin gona da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono shine ya bayyana haka yayin bikin ƙaddamar da irin waken da fara sayar dashi ga manoma, wanda aka gudanar a ranar talata a Kano.

Alhaji Sabo Nanono wanda shugaban cibiyar nazarin bincike kan harkokin noma ta ƙasa farfesa Garba Hamisu Sharubutu ya wakilta ya ce duk da cewa a yanzu Najeriya ita ce ƙasa da ta fi noman wake a duniya, amma abin mamaki akwai giɓin tan dubu ɗari biyar da ake buƙata wanda daga ketare ake shigo da shi.

‘‘Saboda haka sabon nau’in irin waken da ke bijirewa ƙwarin Maruca wadda cibiyar nazarin bincike kan harkokin noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a ta samar da haɗin gwiwar gidauniyar bunƙasa aikin gona ta nahiyar afurka da ke birnin Nairobin Kenya, zai taimaka gaya wajen samar da abinci mai gina jiki ga al’ummar Najeriya,’’ a cewar sa.

Tun farko da ya ke gabatar da jawabi ministan kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar bunƙasa fasahar Biotechnology a Najeriya, farfesa Abdullahi Mustapha, ya ce, nau’in irin waken na SAMPEA-20T yana da matukar alfanu kuma ba shi da illa ga muhalli.

A nasa bangaren gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji ya wakilce shi a wajen bikin Ƙaddamar da nau’in irin waken, ya ce, gwamnatin Kano a shirye ta ke da ta ci gaba da aiki da cibiyoyin bincike wajen bunƙasa aikin gona.

Shi ko jagoran masana kimiyyar da suka gudanar da binciken samar da irin waken na SAMPEA-20T, Dr Muhammad Lawan Umar, cewa ya yi, tun farko halin da manoma su ka shiga sakamakon lalata musu wake da sutsotsin Maruca ke yi, shi ya sanya cibiyar da sauran abokan huldarsu suka fara bincike da aka dauki tsawon shekaru goma ana yi don samar da mafita.

Bikin ƙaddamar wa da fara sayar da irin waken na SAMPEA-20T ga manoma wadda cibiyar bincike kan harkokin noma ta jamiar Ahmadu Bello da ke Zari’a, (Institute of Agricultural research), da haɗin gwiwar sauran abokan huldarsu da suka haɗa da: gidauniyar bunƙasa aikin gona ta nahiyar afurka (African Agricultural Technology Foundation), ya samu halartar dukkannin masu ruwa da tsaki, ciki har da manoma, da kamfanonin sayar da iri.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!