Connect with us

Addini

Sabuwar Shekarar Musulunci: Ganduje ya ayyana litinin a matsayin ranar hutu ga ma’aikata

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana ranar Litinin 09 ga watan Agustan 2021 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata don murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya ayyana Litinin din, da ke zaman 1 ga watan Muharram hijra 1443.

Gwamnan ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa, hutun wani bangare ne na tunawa da sabuwar kalandar Musulunci ta 1443, a don haka an bukaci ma’aikata da su yi amfani da ranar wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!