Connect with us

ilimi

Hutun sabuwar shekarar musulunci bai shafi masu rubuta jarrabawa ba – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce hutun sabuwar shekarar musulunci da ta bayar bai shafi masu rubuta jarrabawar NECO da SSCE ba.

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ce ta fitar da sanarwar mai dauke da sa hannun kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Kiru.

Sanarwar ta bukaci iyaye da daliban da suke rubuta jarrabawar NECO SSCE ta Shekarar 2021 cewa hutun da gwamnati ta bayar na ranar Litinin 9 ga watan Ogusta bai shafi harkar jarrabawar ta su ba.

Saboda haka ana umartar dukkanin daliban da suke rubuta jarrabawar da su tabbatar sun je cibiyoyin su domin ci gaba da rubuta jarrabawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!