Labarai
SACA: kimanin kaso 35 cikin dari masu dauke da cutar HIV ke karbar magani
Babban daraktar a hukumar da ke kula da masu dauke da cuta mai karya garkuwa wato AIDS Sabitu Shanono ya ce kaso 35 cikin dari na masu dauke da lalurar HIV/AIDS dake jihar Kano na amfani da magunguna a fadin jihar.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar shugaban hukumar kuma likita Dr Shanono , ne ya bayyana haka a yayin da yakai ziyara fadar mai martaba sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu a fadarsa.
Dr Shanono da yake kaddamar da watan wayar da kan masu dauke da lalurar ya ce hukumar da ke lura da masu dauke da cuta mai karya garkuwa HIV/AIDS zata fara wannan gangami ne a masarautar Karaye a mako mai kamawa.
Daraktan ya ce gangamin wayar da kan zai bada gwajin da akeyiwa masu juna biyu a asibitocin mata masu juna biyu.
Ya kuma bukaci goyon bayan masarautar Karaye wajen yaki da cuta mai karya garkuwa jiki.
Da yake agana sarkin Karaye Alh Ibrahim Abubakar ya jadadda goyon bayan masarauta domin tabbatar da an rage yaduwar cuta mai karya garkuwa.
Ya kuma bukaci alumma da su tabbata sun hallarci taron domin tantance kansu basa dauke da cuta mai karya garkuwa.