Labarai
Sai gwamnatin Najeriya ta zuba jarin Dala biliyan 10 za ta iya farfaɗo da harkokin lantarki- Adebayo
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce Gwamnatin Tarayya na bukatar zuba jarin dala biliyan 10 a duk shekara, domin farfado da harkar wutar lantarki na tsawon shekaru 10 masu zuwa.
Ministan ya bayyana haka ne a birnin Tarayya Abuja, ya yin wani taron zaman bincike na kwana daya kan kudurin dakatar da karin kudin wutar lantarki da hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta yi, da Majalisar Dattawa ta bukaci a yi Binciken.
A cewar Adelabu, gwamnati na bukatar kashe kasa da dala biliyan 10 a duk shekara nan da shekaru 10 masu zuwa, muddin ana bukatar samar da tsayayyar wutar Lantarki a fadin kasar.
A cewar sa Hakan ya biyo bayan abubuwan da ake bukata na samar da ingantaccen kayan aiki a fannin, amma gwamnati ba za ta iya daukar nauyin hakan ba.
Inda ya kara dacewa dole ne Gwamnati ta sanya fannin ya zama a bude ga masu zuba jari da masu ba da lamuni, don cimma manufar da aka sa a gaba.
You must be logged in to post a comment Login