Labarai
Sakacin mutane ne ke haddasa gobara a lokacin sanyi-Kazeem Oyefola
Hukumar kashe gobara ta kasa reshen jihar kano tace Sakacin da mutane ke yi ne ke haddasa gobara a lokacin sanyi.
Hukumar ta kuma ce kaso tamanin cikin dari na al’umma ba su da ilimin yadda zasu kare kansu daga gobara hakan yasa ake asarar rayuka da dukiyoyi.
Shugaban hukumar Kazeem Oyefola sholadoye ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da hantsi na freedom Radio.
Oyefola yace da mutane na da ilimin yadda zasu kare kansu yayin da gobara ta tashi da zasu iya magance matsalar gobara ba tare da jiran hukumar kashe gobara ba.
“Mafi akasarin gobarar da ake samu iskar gas ce sila domin da yawan masu amfani da shi basa ajiye shi inda ya dace, kazalika basa takatsantsan wajen amfani dashi”.
Kazeem ya kuma ce yana da kyau mutane su samu ilimi a kan yadda ake amfani da kayan kashe gobara don rage asarar rayuka da dukiyoyi.
Sakacin mutane ne ke haddasa gobara a lokacin sanyi-Kazeem Oyefola
Hukumar kashe gobara ta kasa reshen jihar kano tace Sakacin da mutane ke yi ne ke haddasa gobara a lokacin sanyi.
Hukumar ta kuma ce kaso tamanin cikin dari na al’umma ba su da ilimin yadda zasu kare kansu daga gobara hakan yasa aka asarar rayuka da dukiyoyi.
Shugaban hukumar Kazeem Oyefola sholadoye ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da hantsi na freedom Radio.
Oyefola yace da mutane na da ilimin yadda zasu kare kansu yayin da gobara ta tashi da zasu iya magance matsalar gobara ba tare da jiran hukumar kashe gobara ba.
“Mafi akasarin gobarar da ake samu iskar gas ce sila domin da yawan masu amfani da shi basa ajiye shi inda ya dace, kazalika basa takatsantsan wajen amfani dashi”.
Kazeem ya kuma ce yana da kyau mutane su samu ilimi a kan yadda ake amfani da kayan kashe gobara don rage asarar rayuka da dukiyoyi.
You must be logged in to post a comment Login