Labarai
Sama da kaso 77 cikin 100 na masu amfani da man bilicin sun fito ne daga Najeria
Wani bincike da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya gano cewa kaso saba’in da bakwai cikin dari na mata masu amfani da man sauya launin fatar jiki a duniya ‘yan Najeriya ne, wanda kuma hakan ke haddasa mutuwar da dama daga cikinsu sakamakon kamuwa da ciwon koda da hanta da dai sauransu.
Shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan a nan Kano, yayin taron bita na wuni guda da hukumar ta shiryawa ‘yan jarida, domin su fadakar da al’umma illolin sauya launin fata.
Shugabar kuma ta kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki mataki kan masu shigo da mayukan da ke sauya launin fatar.
Wanda suke ganin wannan itace hanya mafi sauki da za’a dakile wannan matsalar a kasar nan.
Rahoton:Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
You must be logged in to post a comment Login