Labarai
Sama da mutane miliyan 13 za su yi fama da karancin abinci a arewacin Najeriya – FAO
Hukumar kula da noma da abinci ta majalisar dinkin duniya da takwararta ta samar da abinci ta duniya sun yi hasashen cewa sama da mutane miliyan goma sha uku za su yi fama da karancin abinci a arewacin Najeriya a cikin watan jibi na Agusta.
Hakan na cikin wani rahoto ne da hukumomin biyu su ka yi wanda ya yi duba kan samar da abinci tsakanin watan Maris zuwa Yuli.
Rahoton ya kuma yi gargadi ga kasashen duniya ashirin wanda ya bukaci jagororinsu da su tashi tsaye don tunkarar matsalar da ke gabansu.
A Najeriya rahoton ya alakanta lamarin da matsalar da rikice-rikice da ke faruwa a kasar wanda a cewar manazartan hukumomin biyu zai taka rawa wajen sanya jama’a da dama cikin rayuwar hannu baka hannu kwarya.
Hukumomin samar da abinci na duniyar sun kuma bayyana damuwa sosai kan al’ummomin da ke rayuwa a yankin arewa maso gabashin kasar nan musamman mazauna Abadam, Dikwa da Guzamala da Kukawa da kuma Marte.
You must be logged in to post a comment Login