Labarai
Sama da mutane miliyan 3 sun yi rijistar katin zaɓe cikin mako 9 – INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ce, mutane sama da miliyan 3 ne suka yi rijistar zaɓe a cikin mako 9 bayan dawo da ci gaba da yin katin a ƙasar nan.
INEC ta bayyana hakan a wani rahoto da ta fitar a Abuja, inda ta ce, mutane miliyan 3 da dubu dari 325 da dari 741 ne suka yi ristar a cikin mako 9.
Hukumar ta kuma ce, a rahoton da ta tattara ya nuna cewa mafi yawa daga cikin mutanen sun buƙaci a sauya musu bayanan su, yayin da wasu suka buƙaci a basu katin na din-din-din da sauran ƙorafe-ƙorafe.
A cewar INEC, mutane dubu 230 sun yi rijisatar ta Internet, yayin da sama da mutane 139 suka je cibiyoyin yin rijistar.
You must be logged in to post a comment Login