Labarai
Fiye da yan Nijeriya miliyan 64 na fama da ƙarancin abinci- MDD
Majalisar dinkin duniya ta ce, yan Najeriya sama da miliyan 64 ne ke fama da matsalar ƙarancin abinci.
Hukumar samar da Abinci ta majalisar dinkin duniya ta kuma ce, mutane miliyan 170 a ƙasashe 19 ba su da isasshen abinci.
Ƙasashen da suka fi fuskantar matsalar sun haɗa da Niger da Mali da Burkina Faso da Guinea da Chadi da Saliyo da Kamaru.
Sauran sun hadar da Liberia da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da Togo da Guinea Bissau da kuma nan Najeriya.
A cewar rahoton ƙarancin abinci a Najeriya ya ƙaru daga kashi 29 zuwa 32 a cikin watanni uku da suka gabata.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login