Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta umarci sabbin wakilai su gabatar mata da shaidar cin zabensu

Published

on

Majalisar dokokin a jihar Kano ta bukaci Zababbun ‘Yan Majalisun jihar da hukumar INEC ta baiwa shedar cin zabe, da su gabatar shedar tasu ga ofishin Akawun majalisar farawa daga yau Alhamis 30 ga watan Maris.

Akawun majalisar Alhaji Garba Bako Gezawa ne yayi wannan kiran ta cikin sanarwar da sakataren yada labaran majalisar Uba Abdullahi ya fitar, aka rabawa manema labarai.

Bako Gezawa ya kuma taya zababbun ‘Yan Majalisun jihar masu jiran gado murnar lashe zaben, tare da yi musu fatan alkhairi.

Rahoton:Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!