Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

 Samar da fasahar 5G zata bun kasa tattalin arzikin Najeriya- Dakta Abdurrazaq Fagge

Published

on

Masana tattalin arzikin sun fara bayyana ra’ayinsu kan batun samar da fasahar 5G.

Shugaban sashen kimiyyar tattalin arzikin kasa na Jami’ar Yusif Maitama Sule a nan Kano Dakta Abdurrazaq Fagge ya ce asamar da fasahar zai taimakawa tattalin arziki.

Dakta Abdurrazaq Ibrahim ya bayyana hakane a zantawarsa da Freedom Radio.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da gwamnatin tarayya ta ayyana fara amfani da sabuwar fasar sadarwa ta 5G a shekarar 2022.

Ya ce sabon tsarin zai kuma bunkasa yadda hada-hadar kasuwanci a bangaren tattalin arzikin kasar nan.

“Sakamakon yadda yanzu mutane da dama sun koma amfani da shafukan sada zumunta, hakan zai sa sabon tsarin na 5G ya farfado da durkushewar karfin Internet da ake dashi”.

“Idan ka duba a yanzu karfin Internet din ba shi da karfi a wasu jihohin, in ban da jihar Lagos da Fatakwal da kuma birnin tarayya Abuja,” inji Dakta Abdurrazaq Fagge.

Ya kuma ce yawan hada-hadar da za’a samu tsakanin masu ziyartar shafikan sada zumunta zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma samun kudaden shiga.

Gwamnatin tarayya ta ayyana cewa kasar nan ta yi shirin fara amfani da fasahar 5G daga watan Janairun shekarar 2022 mai zuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!