Labarai
Samar da Yan sandan jihohi zai magance rashin tasaro- Gwamnonin Arewa

Kungiyar gwamnoni jihohin Arewacin Najeriya, ta bayyana cewa samar da yan sandan jihohin zai taimaka musamman wajen magance matsalar rashin tasaro da ke addabar kasar, musamman ma a shiyyar Arewa.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a jawabinsa yayin taron da kungiyar gwamnonin Arewa ta shirya kan lalubo bakin zaren matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin.
Ya kuma bayyana cewa za su ci gaba da bai wa gwamnatin tarayya hadin kai domin magance matsalar rashin taro a dukkan fadin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login