Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Samari masu ƙwacen waya sun shiga hannu a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kama wasu matasa 31 waɗanda ake zargi da ƙwacen waya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
DSP. Kiyawa ya ce, ana zargin matasan ne da tare hanya a daren Asabar a daidai mahaɗar titin Ɗanagundi da ke ƙaramar hukumar Birni da Kewaye inda suka riƙa karɓe wayoyi a hannun mutane.
An samu matasan da babura guda huɗu da wuƙaƙe manya da ƙananan da kuma miyagun ƙwayoyi a cewarsa.
Sai ku biyo mu a shirye-shiryen mu na gaba, domin jin cikakken labarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!